Wannan ma na zuwa ne yayin da dubun wasu masu garkuwa da mutane ke cika a jihar Adamawa.
Yanzu haka tuni aka soma shirye shiryen sallar azumin bana wato karamar sallah kamar yadda ake kira a wasu wuraren, inda a bana jama'a ke cewa sallar ta zo musu a wani yanayi na rashin masu gidan rana.
Kawo yanzu tuni hukumomin tsaro suka shirya tsaf a jihohin biyu don kare rayuka da dukiya yayin gudanar da bukukuwan sallar kamar yadda kakakin rundunar tsaron farin kaya ta Civil Defense a jihar Adamawa Suleiman Baba ya yiwa Muryar Amurka bayani.
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa, da yake nunawa manema labarai wadanda aka kaman, kwamishinan yan sandan jihar Adamawa Audu Madaki ya ce sama da mutum talatin aka cafke da suka hada da yan fashi, da masu garkuwan da kuma yan jagaliyar yan shila da yanzu ke addabar jama'a.
Ita ma rundunar yan sandan jihar Taraba a sanarwar data fitar ta ce tuni aka baza jami'an aiki da cikawa domin tabbatar da kare rayuka.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5