Kungiyoyin rajin shugabanci nagari da wanzar da dimokaradiyya na gudanar da tarukan mahawara domin samar da wani daftari da za su bibiyi yadda gwamnatocin za su magance matsalolin da ke damun al’uma a sassa daban daban na kasar.
Hakan na zuwa ne, yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan rantsar da sabuwar gwamnati a matakan tarayya da na jihohi a Najeriya a ranar 29 ga watan gobe na Mayu.
Kungiyar wayar da kan Jama’a akan harkokin dimokaradiyya ta Organization for Community Civic Engagement hadin gwiwa da kungiyar National Endowment for Democracy suka shirya taron mahawarar tare da tattaunawa akan batutuwan da suka shafi makomar rayuwar al’uma a matakai daban- daban.
Masana da masu sharhi akan fannoni daban-daban ne suka gabatar da Makala.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mata ke korafi kan yadda maza ke mamaye madafun iko a fagen siyasar najeriya.
Babban fata dai shi ne wannan sabon salon yunkuri na kungiyoyin ya haifar da sakamako mai alfanu.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari domin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5