An Fara Binciken Tashin Gobarar Gidan Yari a Kamaru

Hukumomi a Kamaru sun fara binciken wutar da ta tashi a babban gidan Yarin dake Doula mai tashar jirgin ruwa da tayi sanadiyar kwantar da wasu fursinoni uku a asibiti da munanan raunukan kunar wuta.

Wani jami’in kashe gobara yace wasu ma’aikatan kwana kwana biyu sun ji rauni a jiya Alhamis yayin da suke kokarin wutar da ta tashi a gidan yarin News Bell a birnin hada hadar.

Ma’aikatan kashe gobara sun hana wutar yaduwa zuwa wasu gine gine a unguwar mai yawan jama’a dake kusa da gidan Yarin.

Sai dai ba a gano musabbanin tashin gobarar ba ko kuma tashin wutar na da alaka da yawan cunkoson jama’a a gidan Yarin.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama ciki har da Amnesty International, sun ce cunkoson jama’a da rashin tsafta da rikici sune kalubalen da suka addabi gidajen Yarin Kamaru.