Majalisar ta dora wa kwamitin nauyin binciken zargi da ake yi cewa ba a bin tsari wajen daukan Ma'aikatan gwamnati inda ake ganin akwai zamba, cin hanci da rashawa da kuma cin zarafi ta fanin yin amfani da kudi. Shugaban kwamitin wanda ke wakiltan mazabar Pankshin Kanke Kanam ta JIhar Pilato Yusuf Adamu Gagdi ya bayyanawa Muryar Amurka cewa, kwamitin zai yi aiki tukuru wajen binciken ma'aikatu da hukumomin gwamnati sama da 800
Gagdi ya ce daukar ma'aikata yana da tasiri a aikin gwamnatin domin ta haka ne ta ke yin abubuwan da suka shafi al'umma, daidaita al'umma, rage radadin talauci da kuma kara duba yadda gwamnati ta ke asarar biliyoyin kudade a duk wata ga ma'aikatan bogi da kuma biyansu ba a bisa ka'ida ba. Gagdi ya ce badakala ce da ta shafi fanoni daban daban na rayuwar al'umma irin su makarantun gaba da sakandare da sauransu. Gagdi ya ce dole Majalisa ta duba domin kar kasar ta cigaba da yin hidima ta ma'aikata da ba su cancanta ba.
To sai dai ga masani a tsangayar zamantakewan dan Adam da gudanar da mulki Abubakar Aliyu Umar ya ce dole Majalisa ta sauya irin salon binciken da ta dade ta na yi. Abubakar ya ce tun zamanin Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ake ta bincike a Majalisar amma ba ya tasiri. Abubakar ya ce Majalisa ta kan yi irin wannan Kwamitocin ne domin taimakon 'ya'yanta, ba wai taimaka wa kasa binciken yake yi ba. Abubakar ya ce yana fata a wanan Majalisa ta 10 za a ga banbanci a ayyukan da suka tsara.
Amma ga dan Majalisa mai wakiltan Maiyama da Kokobese na Jihar Kebbi Salisu Garba Koko ya ce wannan bincike abu ne da zai haifar wa kasa da mai ido domin zai ba kowa daman a yi da shi babu wani banbanci domin al'amuran kasa su tafi daidai. Salisu ya ce aikin Majalisa ne yin irin wannan bicike domin a samu daidaito a harkar gudanar da kasa.
Kafin wannan Kwamiti ya fara bincike, Majalisar ta amince Gwamnati ta daga takunkunmin da ta dora a fanin daukan kanana da matsakaitan ma'aikata a hukumomi da ma'aikatun gwamnati saboda a kawo saukin wahalhalun da matasa marasa aikin yi ke sha.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5