An Fara Bada Rigakafin Cutar Kwalara A Mozambique

An fara gagarumin aikin alluran rigakafin cutar kwalara a kasar Mozambique don hana yaduwar cutar daga juyawa zuwa annoba mai tsanani.

Ma'aikatar Lafiya ta kasar Mozambique ta tabbatar da cewa fiye da mutane 1,400 suka kamu da cutar kwalara, inda har mutane biyu sun mutu a birnin Beira, wanda mummunar guguwar Cyclone Idai tafi shafa.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO a takaice tare da Asusun kananan yara na majalisar dinkin duniya ke jagorantar yaki da cutar.

A cikin kwanaki biyar masu zuwa, hukumomin biyu sun shirya bada alurar riga kafin cutar ga kusan mutane 900,000 a garin Beira da wuraren da ke kewaye dashi.