An Fara Aikin Gwajin Cutar Hawan Jini A Kano, Ogun

An kaddamar da aikin gwajin cutar hawan jini a wasu cibiyoyi a jihohin Kano Da Ogun a Najeriya.

An kaddamar da shirin yaki da cutar hawan jini a Najeriya, wadda ke neman zama ruwan dare a tsakanin tsofaffi da matasan kasar.

Cutar hawan jini na da nasaba da al'amurran rayuwar yau da kullun ga wasu.

Shirin wanda aka fara shi a mataki na gwaji, inda za’a fara gudanar da shi a jihohin Kano da Ogun, kafin daga bisani a duba yiwuwar fadada shi zuwa sauran sassan kasar.

Hukumar lafiya ta duniya da hadin gwiwar kungiyar "Resolved to save lives" kana da ma’aikatar lafiya ta Najeriya suke daukar ragamar shirin. Inda wasu da suka shiga cikin shirin suke bayyana musabbabin ciwon ya same su.

Daya daga cikin su, ta bayyana cewar tun bayan rasuwar mai gidanta wanna cutar ta hauwan jini ta same ta, a inda dayar kuwa Binta Umar ke cewa, ta kwashe kimanin shekaru 15 da wannan cutar, tun wajen haihuwa wannan cutar ta samota. Ciwon ya kan shafi duk sauran bangaroroin jikinta.

Dr Imam Wada Bello, daraktan kula da ayyukan kananan Asibitoci da cibiyoyin shan magunguna a hukumar kula da Asibitoci ta jihar Kano, ya fayyace alkibilar shirin bayan kaddamar da shin.

Ciwon hawan jini kan kashe mutane cikin ruwan sanyi batare da an ankara ba, a lokutta da dama mutane kan samu ciwon mutuwar rabin jiki, wanda hawan jini ke haifarwa, amma a wanna cibiyar yanzu za'a dinga yin gwaji don tabbatar da masu dauke da ita da kuma basu kulawa da ta dace.

Haka shi ma shugaban Ofishin Kano na hukumar lafiya ta duniya Dr Bashir Abba ya yi bayani akan rawar da hukumar ta WHO zata taka wajen aiwatar da shirin.

Hukumar Lafiya ta duniya za ta samar da masana da hada kan duk masu ruwa da tsaki a fannin cutar ta hawan jini. Za kuma a tabbatar da cewar an samar da kayan gwaji a duk cibiyoyin da aka samar a ko ina, mutane za su biya kudade kadan don siyan magani.

Alkaluma daga hukumomin kiwon lafiya a jihar Kano na nuna cewa, kashi 35 cikin dari na masu dauke da ciwon zuciya suna dauke da cutar hawan jini.

Ga rahoton da Mahumud Ibrahim Kwari ya hada muna cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Aikin Gwajin Cutar Hawan Jini A Kano, Ogun