Gwamnatin Najeriya ta yi nassarar maido da ‘yan kasar 69 daga kasar Lebanon, 50 daga cikinsu ‘yan mata ne wadanda aka yi safarar su zuwa kasar, yayin da sauran 19 kuma suka makale saboda barkewar cutar COVID-19.
Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ake safarar bil adama musamman mata da kananan yara wadanda ake tilasta su yin aikatau ko karuwanci don samun kudi, da mafi akasari ake fita da su ta barauniyar hanya zuwa wasu kasashe a yankin Turai ko Larabawa.
Gwamnatin kasar ta ce ta sami goyon baya daga gamnatin kasar Lebanon da ‘yan kasar mazauna Najeriya wajen dawowar wadannan mutane su 69 a Najeriya. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Ferdinard Nwonye, ya bayyana cewa, a yanzu haka an kebe mutanen da aka dawo da su daga Labenon na tsawon kwanaki 14 kamar yanda hukumomin lafiya suka ba da umarni, domin kariya da kuma dakille yaduwar cutar COVID-19.
Hukumar NAPTIF wacce ke da alhakin yaki da safarar mutune a Najeriya ta ce za ta ba su horo da ilimi don su amfani kansu da kasar su ta asali.
Wani rahoto na Majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa a duk shekara ana safarar dubban ‘yan Najeriya da wasu ‘yan kasashe Afirka wadanda ake musu alkawari samun aiki a kasashen yakin Turai ko Asiya, amma daga karshe a tilasta musu yin aikatau ko siyar da mutuncunsu don samun kudi.
Kakakin hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta NIDCom Rasheed Balogun ya ce, akwai hadin gwiwa tsakanin hukumarsu da ta NAFTIP, don haka bayan kammala wa’adin kwanaki 14 na kebe mutanen da aka dawo da su daga Lebanon, kamar yanda aka saba za’a tantace su, kana za’a yi amfani da labarin da su ka bayar don yin gargadi ga sauran ‘yan kasar da ke sha’awarar zuwa kasashen waje da nufin samun rayuwa mai inganci, sannan kuma a basu horo bisa kwarewarsu na sana’ar hannu.
Ya zuwa yanzu Gwamnatin Najeriya ta yi nasarar maido yan kasarta 265 daga kasashen yakin larabawa, 253 daga Birtaniya, sai kuma 160 daga Amurka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5