An Daure Wasu Na Hannun Daman Tsohon Shugaban Kasar Algeria

Wata karamar kotun soja a Algeria ta ce an gudanar da bincike a kan wani dan uwa kuma na hannun daman shugaba Abdelaziz Bouteflika da wasu manyan sojoji biyu da suke jagorantar sashen leken asirin kasar a baya a kan cin amanar kasar kuma an daure su a gidan yari.

Wata sanarwa a jiya Lahadi daga kotun dake Blida a kudancin birnin Algiers na cewa, mai shigar da karar ne ya bada sunan alkalin da zai gudanar da binciken shari’ar.

A shekaran jiya Asabar ne aka tsare Said Bouteflika da Mohamed Mediene da aka fi sani da Toufik da kuma Athmane Tartag da suka jagorancin ma’aikatar leken asirin kasar zuwa karshen watan da ya gabata.

Wadannan mutane uku, kusoshi ne a zamanin mulki Bouteflika wanda ya yi murabus a ranar biyu ga watan Afrilu daga shugabancin kasar.

Wani hoton bidiyo da telbijin kasar ya nuna, an ga mutanen uku suna hawan matattakalar ginin kotun.