Cin zarafin kananan yara yana kara samun gindin zama a arewacin Najeriya, duk da fafatukar da kungiyoyi da hukumomi ke yi don magance matsalar.
A cikin wannan shekara ta 2020 an samu mutane da aka kulle tsawon lokaci a jihohin Kano da Kebbi, yanzu kuma abin yazo Sakkwato domin an gano wani yaro da aka daure tsawon lokaci matar mahaifinsa na azabtar da shi.
Lamarin ya faru ne a unguwar Helele dake cikin karamar hukumar Sokoto ta arewa inda aka tarar da yaro dan kimanin shekara 12 an daure shi a gungumen icce matar mahaifinsa tana azabtar da shi.
Ayarin jami'an kiyon lafiya da ke zagaye gida-gida suna bayar da maganin zazzabin cizon sauro suka tarar da yaron daure, lokacinda suka shiga gidansu.
Mataimakin daraktan kula da jin dadin jama'a kuma jami'in kare hakkin mata da kananan yara na karamar hukumar ta Sakkwato ta arewa, Bello Ladan yace suna samun rahoton suka je domin su bincika kuma suka tarar gaskiya ne.
To ko wane laifi ne yaron mai suna Nuhu ya aikata har aka yi masa wannan hukunci, Rabi ita ce matar mahaifin yaron wanda tuni ya rasu, kuma ita ce ke kula da yaron.
Akwai alamun cewa lallai yaron ya samu matsalar kwakwalwa domin kuwa ba a gane maganarsa.
Kimanin wata biyu yanzu da irin wannan matsalar ta faru a jihohin Kebbi da Kano kuma yanzu haka masu hannu a lamarin suna fuskantar shari'a.
Bincike ya tabbatar da cewa ko a Sakkwato an samu faruwar makamanciyar wannan matsala a unguwar Minannata, da makarantar Malam Dan Gombe da kuma garin Illela.
Yanzu dai jami'an tsaro na civil defence sun gayyato Dangin mahaifin yaron domin ci gaba da bincike.
Ga Muhammad Nasir da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5