Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye shiryen babbar Sallah,rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro domin ganin an gudanar da bukukuwan sallar cikin tsanaki.inda aka kara baza jami’an tsaro a cikin shirin ko ta kwana.
Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro nne aka tanadar a jihohin Adamawa da Taraba gabanin wannan biki na Sallah,da suka hada da sojoji da,yan sandan da kuma jami’an hukumar tsaron farin kaya da ake cewa Civil Defense,inda suke karade manyan tituna don tabbatar da an bi doka da oda.
Da yake karin haske game da matakan da aka dauka gabanin bikin Sallan da za’a soma Juma'a ,Kakakin rundunan jami’an tsaron farin kaya a jihar Adamawa Suleiman Baba,ya ce an dau matakin ne don kare rayuka da dukiyar jama’a.
To sai dai yayin da jami’an tsaro ke daura damarar shirin ko-ta-kwana,suma yan kasar na can suna fama da sayayya don fuskantar sallar,koda yake akwai wani hanzarin da ba gudu ba na tashin farashin kayayyakin masarufi, kamar yadda yan kasuwa da masu say eke kokawa.
A baya dai bukukuwan Sallah dana kirsimeti kan zama tubulin sada zumunci a tsakanin kirista da Musulmi. Mr Vandi Kasu dake mataimakin sakataren kungiyar sasanta Musulmi da kirista ta Christians and Muslims Peace Intiative,ya bayyana tanadin da yayi don taya Musulmi murna.
Your browser doesn’t support HTML5