An Dauki Tsauraran Matakan Tsaro A Jalingo

Gwamnan Taraba Danbaba Suntai

Yayin da Jihar Taraba ke jiran dawowar gwamnan gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakan tsaro domin halin ko ta kwana.
Yayin da Jihar Taraba ke dakun jiran dawowar gwamna Danbaba Suntai wanda ya kwashe fiye da watanni goma yana jinya a kasashen Jamus da Amurka, gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakan tsaro a Jalingo babban birnin jihar.

Rundunar 'yansandan jihar tun can farko ta fitar da sanarwa inda ta yiwa jama'a kashedi. Ta ja masu kunne tana gargadinsu cewa ba zata bari kowa ya fake da dawowar gwamna Danbaba Suntai ya tada hankali ba. Sai dai da alamu mutanen garin Jalingo na cikin wani halin shirin gagarumin biki domin tarabar gwamnansu yayin da jami'an tsaro suka mamaye garin.

Mutanen da aka zanta da su sun fadi albarkacin bakinsu gameda labarin dawowar gwamnan. Wani ya ce alamar zai dawo din shi ne yawan jami'an tsaro dake sintiri koina a birnin. Wani kuma dan siyasa godiya ya yiwa Allah cewa gwamna Suntai zai dawo. Ya ce zasu yi masa maraba mai kyau tare da biki. Ya kira 'yan siyasa su mayarda zuciya nesa su bar ban-bancin addini ko na kabilanci domin cigaban jihar da ma kasar gaba daya. Shi kuma wani limamin Krista cewa ya yi lokaci ne yayi da zasu karbi Danbaba Suntai da murna. Ya yabawa mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umaru wanda ya ce ya rike jihar da adalci ba tare da munafinci ba ko wata manufa.

A nasa jawabin mukaddashin gwamnan Garba Umaru godiya ya yi wa Allah cewa gwamnan zai dawo. Ya ce komi na Allah ne. Shi dama ya rike ma gwamnan mukaminsa ne. Idan Allah ya dawo da shi sai ya cigaba da milkinsa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Dauki Tsauraran Matakan Tsaro A Jalingo-2.50