Daga cikin matakan tsaron da hukumomin tsaron Nigeria ke dauka harda rage kaiwa da komowar ‘yan Nigeria da rage zirga-zirgar motoci a kan tituna. Jami’an tsaron Nigeria sun kuma yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana neman janyo cikas a ranar zaben sai ya kuka da kansa. ‘Yan Nigeria na kukan yawan fadace-fadacen ‘yan bangar siyasa, yanzu haka kuma rundunar ‘yan sandan Nigeria ta fara binciken rahotannin da ake samu na tashe-tashen bom a wasu wuraren. A birnin Kaduna da Kewaye an sami rahoton kashe wani a daren Alhamis lokacin da bom din da yake kokarin danawa yab tashi a hannunsa. Jami’an hukumar zaben Nigeria sun bada hujjar dage zaben na ‘yan majalisar tarayya ne saboda karancin kayan aiki, amma da alamar al’amura zasu gyaru im banda dan abinda ba’a rasa ba kamar karancin takardun kuri’a a wasu sassan kasar da hakan yasa aka jingine gudanar da zaben na ranar Asabar a wasu jihohin.
An Dauki Kwararan Matakan Tsaro A Jajiberen Babban Zaben Da Za’a Fara Daga Ran Asabar A Nigeria
Asabar ce idan Allah ya kaimu ake zaben ‘yan majalisar dattawa da ta wakilan Nigeria. Zaben da ake dage yinsa a makon jiya.Juma’a ce Ma’aikatar harkokin gida a Nigeria ta bada sanarwar rufe dukkan kan iyakokin Nigeria, sannan aka tuttura ‘yan sanda domin zuba ido da gadin dukkan rumfunan zaben da za’a jefa kuri’a.