An Damke Wata Matashiya Mai Kokarin Sayarda 'Ya'Yanta

Hukumar hana fataucin mutane NAPTIP, ta damke wata matashiya mai shekaru ashirin da biyar mai suna Ali Odinaka, wace ake zargi da kokarin sayarda ‘ya’yan ta har su ukku.

Odinaka, ‘yar asalin Ezilo dake cikin karamar hukumar Ishielu, dake jihar Ebony, a tarayyar Najeriya, an damke ta ne baya da aka tseguntawa ‘yan Sanda, niyyarta na son sayarda ‘ya’yanta bayan da ta tuntubi wata mata mai aiki a wani gidan cin abinci cewar ta nemamata mai fataucin mutane.

Da take bada tabbacin labarin kakakin hukumar hana fataucin mutane a jihar ta Ebonyi, Florence Onwa, ta ce wace ake zargin ta yanke hukunci sayarda yaran ne baya taga cewa bata da karfin rike ‘ya’yan nata tunda mijinta ya kaurace masu.

Da yake tsokaci akan batun shugaban sashen dake kula da yara na ma’aikatar mata da zamatakewa Godwin Igwe, yayi kira ga jama’a, da masu hannu da shuni, dasu taimakawa wanna mata domin kula da ‘ya’yanta.

Itama da take bayani tace ci da kanta yana yimata wuya tunda mijinta ya kaurace masu a watan Afrilu, shine dalilin da ya sata yanke wannan shawarar.