An Damke Wasu Matasa Ukku 'Yan Danfarar Yanar Gizo

Rundunar ‘yan Sandan Najeriya, ta cafke wasu matasa wadanda ake zargi da dafarar wani dan kasuwa mai sana’ar gidaje a Legas.

Kamar yadda jaridar Punch, ta ruwaito, matasan Olisa Oyegbuka, mai shekaru 28, Ifeannacho Kingsley, mai shekaru 27, da Ujumwa Aniemena macen dake cikinsu ita kuma mai shekaru 33, sun yin kutse cikin email, din dan kasuwan ne.

Inda suka yi sojan gona suka aike da sako suka bukaci a tura wasu kudade cikin wasu ajiyar banki .

An gano almundahanar ne bayan da banki da aka kwashe kudaden suka aike da sako ga mai ajiyar shi kuma ya nemi bayanin dalin kwasan kudaden.

Su dai wadannan matasa an damke su ne a gari Awka, a jihar Anambra, an kuma gano cewa wadannan matasa suna ciki wani gungun wasu ‘yan damfara da suka shahara wajan yin kutse cikin email din mutane sun yi masu barna.

A ranar 24, ga watan Oktoba sun kwashe Naira 800,000, ranar 27, ga watan Oktoba sun sake kwasan Naira 530,000, sannan a ranar 1, ga watan Nuwamba, suka kwashe Naira 720,000, ranar 2, ga watan Nuwamba, suka sake bada umarin a tura Naira 850,000, jimilar kudaden da suka kwasa dai ya kama Naira miliyan 3,800,000.

Kakakin rundunar ‘yanSandan jihar Legas, SP Dolapo Badmos, ta gargadi masu aikata irin wannan laifuffuka a jihar Legas, daga wasu jihohi cewa duk inda suke rundunar zata zakulosu.