WASHINGTON, DC —
Jami’an ‘yan Sanda na masamman karkashin ofishin sufeto janar na ‘yan Sandan Najeriya, sun damke wani gungun wasu masu satar mutane domin amsan kudin fansa a Fatakwal fadar Gwamnatin jihar Rivers.
Wadanda aka kama matasa tara ne Daniel Gabriel(33), Alaso Igodo (25), Akeodi Aselemi (34), Ayibinmotei Livinus (25), Anikuroka Marshal (33) Biebele Elijah (34), Efiye Anda (34), Daniel Lessor (31) and Isaac Reuben (27) dukkan su mazauna Fatakwal ne.
Jami’an na ‘yan Sandan sun sami damar damke wadannan bata gari ne a wani samame na awowi biyar da suka kaddamar.
Wadannan matasa dai suke da alhakin duk sace sacen mutanen da ake yi a unguwanin GRA Phase 2, yankin Borokiri da Woji, a birnin Fatakwal.