Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gurfanar da wani kurma Abass Hamed, mai shekaru ashirin da ukku, gaban kuliya a bisa zargin fatauci miyagun kwayoyi.
Mai gabatar da kara na hukumar ta NDLEA, Mr. Jeremiah Aeran, ya fadawa kotu cewa an cafke wanda ake zargi ne akan titin Agege Motor road, a Legas.
Ya ce a sami kilo gram daya na tabar wewe, da yake saidawa a hannunsa, a cewar ma gabatar da kara ya ce hukumar ta dade tana fakon Hammed, kafin dubunsa ta cika a cafke shi.
Laifin ya sabawa sashe na 11, sakinlayi na 30, na kundin laifuffukan hukumar ta NDLEA,na shekara ta 2004, a cewar mai gabatar da karar, daga bisani kuma ya roki kotu da ta dage karar.
Alkalin kotun mai shara’a Jude Dagat, ya tsayarda ranar 5 da 7, ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da za’a sake sauraren karar.