An Damke Matasa Masu Yiwa Fina Finan Najeriya Zagon Kasa

Hukumar tantace fina finai ta Najeriya, ta damke wasu matasa uku, masu yin kan Ungulu da Zabo, da fina finan jaruman Najeriya.

Matasan Ndu Calestine, Okechukwu Ikuagwu da Austine Ugogkwe, an damke su ne dangane hannu dumu dumu da suke dashi a harkar fina finan na algus da kuma satar fasahar masu fina finan.

An kama su da fina fina da kayan aiki wadanda kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan hamsin (50M), a kasuwar Alaba, dake birnin Legas.

Kamen ya zo ne biyo bayan korafe korafe daga masu sana’ar sayarda fina finai daga arewacin Najeriya, wadanda suka kasance abokan harkar wadannan bata gari masu son maida hannun agogo baya.

Fina finan da na’urar da suke amfani da wajan gurza fina finan dasu kansu suna hannun ‘yan Sanda a “Area E" dake Legas.