An Damke Kasurgumin Dan Ta'addar Daji, Kwaire

Shugaban 'Yan Ta'addar Daji Kwaire

A wani cigaba a yaki da 'yan bindiga, jami'an tsaron Najeriya, wadanda ke kara fuskantar matsin lamba daga al'ummar kasar da ke bukatar su kara kaimi wajen yaki da miyagu, sun kama kutunkun dan ta'addar dajin da ya dade ya na gasa ma jama'a aya a hannu.

A Najeriya, yayin da jama'a ke ta kokawa akan matsalolin rashin tsaro, su kuwa jami'an tsaro sun himmantu wajen yin iya kokarinsu don dakile ayukkan miyagun, kuma wasu lokuta sukan samu sa'a yayin da wasu lokuta kuma abin ya kan basu ruwa.

wannan karon jami'an tsaron 'yan kasa na 'civil defence' sun yi nasarar damke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ya addabi sassan Najeriya, har ma wasu kasashen Afirka, mai suna Alhaji Kwaire.

Mahukunta dai sun jima suna cewa suna bakin kokarinsu wajen magance matsalolin duk da yake har yanzu matslolin basu karewa, amma kuma wasu lokuta jami'an na samun galaba, kamar wadda jami'an tsaron 'yan kasa suka samu a jihar Sakkwato na damke wannan kasurgumin mai gakuwa da mutane mai suna Alhaji Kwaire.

Kumandan rundunar a Sakkwato, Muhammad Sale Dada, shi ne ya jagoranci aikin kame wannan babban dan ta'addan.

Duk da yake wanda aka kaman ya ki aminta da cewa shi jagoran barayi ne, amma dai ya ce ya saba amfana da kayan satar.

To sai dai wanda aka kama su tare, Buba, ya ce sun jima cikin wannanlalurar.

Masana lamuran tsaro a Najeriya sun jima suna tsokaci akan yadda ake kama masu laifi amma ba a hukumta su, abinda ya sa aka tambayi kumandan rundunar ko suna bin karar wadanda suke kamawa har a yi musu hukunci domim kar kokarinsu ya tafi a banza, inda ya ce su na iaya kokarinsu.

Matsalolin rashin tsaro dai sun dabaibaice sassan Najeriya, sun daidaita yankuna tare da kassara jama'a duk da yake mahukunta na kokarin samo bakin zaren warware matsalolin a cewarsu.

Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

08-12-22 Kamun Alhaji Kwaire.mp3