An Dakatar Da Wasu Jami'an Gwamnatin Tarayyar Najeriya Daga Bakin Aiki

  • Ladan Ayawa

EFCC

Kakakin Ministan tarayyar Abuja Abubakar Sani yayi wa wakilin sashen Hausa Hassan maina Kaina dalilin wannan dakatarwan.

‘’Ba shakka wadannan jamiaan an dakatar dasu ne sabo da irin zarge-zargen da ake musu

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, ta gurfanad dasu gaban kotu tana zargin su.

Kasan shi jamiin gwamnati yana iya gudanar da ayyukar sa kamar yadda doka ta tanadar, to kuma a duk lokacin da aka samu akasin haka, to kaga za a dauki matakai ire-iren wadannan, to wannan yakai ga har hukumar EFCC ta shigo cikin wannan batu.

Hukumar babban birnin tarayya ta yi haka ne, wato dakatar dasu domin ta baiwa hukumar ta EFCC cikaken damar gudanar da ayyukan ta.

Shiko Barister Aliyu Abdulahi lauya ne dake zaune a Abuja ga kuma abinda yake cewa game da wannan dakatar da maaikaran.

Ga HassanMaina Kaina da Karin bayani 2’04

Your browser doesn’t support HTML5

AN DAKATAR DA WASU JAMIAAN GWAMNATIN TARAYAR NAJERIYA BAKIN AIKI