Hukumar da ke shirya gasar La Liga a kasar Spain ta ba da hutu a gasar, domin ba da damar yin shagulgulan bikin Kirsimeti da kuma na sabuwar shekarar 2019.
A ranar Lahadi 23 ga watan Disamba 2018, aka kammala buga wasannin mako na 17, inda aka fafata a wasanni guda uku.
A saman teburin mako na 17, Barcelona ce take matsayi na daya da maki 37, sai Atletico Madrid ta biyu da maki 34, sai kuma Sevilla a matsayi na uku da maki 32, ita kuwa Real Madrid tana da maki 29, a matsayi na hudu.
Sai dai Real Madrid tana da wasa daya da za ta yi tsakaninta da Villarreal sakamakon ta buga gasar cin kofin Zakarun Nahiyoyin Duniya (World Club Cup) da aka yi a Abu Dhabi, kuma ta lashe karo na uku a jere kenan.
Villarreal da Real Madrid za su fafata a ranar Alhamis 3 ga watan Janairun 2019.
Hukumar ta ce za a ci gaba da fafatawa a gasar ta La liga mako na 19 a ranar 6 ga watan Janairun 2019.
Kungiyar kwallon kafa ta Huesca ita take kasan teburin da maki 8 banbancin maki 5 tsakanita da Rayo Vallecano, mai maki 13.