Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta dakatar da shirinta na haramtawa masu Adaidaita Sahu bin wasu manyan hanyoyin birnin.
Shugaban hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa ta KAROTA, Baffa Babba Danagundi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Laraba.
"Gwamnati ta amince adaidaita sahu, su ci gaba da bin wadannan tituna har zuwa lokacin da za a tabbatar kowane tsari ya kammala.” In ji Danagundi
Gwamnatin jihar ta Kano a baya ta kafa dokar hana zirga-zirgar masu adaidaita sahu ne bayan da ta samar da motocin safa-safa na daukar fasinja.
“Kamfanin da suke gudanar da sufurin wannan aiki, ba su gama shiryawa yadda al’uma ba za su samu radadi na rashin samun abin hawa ba.” shugaban na KAROTA ya ce.
A ranar farkon makon nan hukumar ta KAROTA ta fitar da wata sanarwa, wacce ta takaitawa masu Adaidaita Sahun bin wasu manyan tituna.
Titunan sun hada daga Ahmadu Bello Way zuwa Gazawa da Tal’udu zuwa Gwarzo Road.
Baburan A Daidaita Sahu masu kafa uku, sun kasance kaso mafi tsoka da al'umar jihar ta Kano ke amfani da su wajen gudanar da harkokin zirga-zirgarsu.