'Yan tawayen Rohingya da ke kasar Myanmar sun yi kiran da a tsagaita wuta na tsawon wata guda tun daga jiya Lahadi, saboda kayan tallafi su samu kaiwa ga wadanda tashin hankalin ya rutsa da su.
Mayakan kungiyar 'yantawaye ta Arakan sun kaddamar da hare-hare kan sansanonin 'yan sanda da na sojoji a karshen watan jiya, al'amarin da ya kai ga raba mutane sama da 300,000 da muhallansu.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Asabar kungiyar ta bayar da tabbaci ga kungiyoyi agaji da cewa su, a tabakinta, "dawo da aikin agajin da su ke yi ga dukkannin wadanda abin ya rutsa da su, ba tare da la'akari da addini ko harshe ba, a tsawon wa'adin tsagaita wutar."
Jiya Lahadi kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin kasar Myanmar da dana bama-bamai da gangan a kan hanyoyin da 'yan gudun hijirar Rohingya ke wucewa zuwa kasar Bangladesh.