An Dakatar Da Ayyukan UNICEF  a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Shugaban Asusun UNICEF Na Maiduguri, Mr. Geoffrey Ijumba

Rundunar sojin Najeriya, ta dakatar da ayyukan Asusun Tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a yankun arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimakawa darektan yada labarai, Col. Nyema Nwachukwu, ta nuna cewa, asusun ba ya gudanar da ayyukan da ke gabansa.

Sanarwar ta ce “daukan wannan mataki ya zama dole, lura da cewa asusun ya yi watsi da ayyukan da ya kamata ya gudanar na kula da yara kanana da taimaka wa mutanen da suka tagayyara, a maimakon haka, sai ya mayar da hankalinsa kan horar da mutane kan yadda za su rika tattaro bayanan sirri da ke kawo cikas ga ayyukan yaki da ake yi da ‘yan ta’adda.”

Rundunar sojin ta Najeriya ta kumace asusun yankan yi zargin da ba shi da tushe kan cewa dakarun Najeriya na cin zarafin mutane, kamar yadda jaridar Premium Times da ake wallafawa a yanar gizo ta bayyana.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labari asusu na UNICEF bai ce uffan ba kan wannan mataki da aka dauka akansa.