WASHINGTON, DC —
Gwamnatin jamuhuriyar Nijar, ta daidaita da Malamanta na kwanteragi dasuke bin Gwamnatin kasar kudaden albashi na watanni da dama.
Ministan ilimin kasar Nijar Dr. Idi iliyasu Mainasara, ne ya kara jaddada hakan a shirin mu na yau da gobe.
Ministan yana mai cewa gwamnatin Nijar, zata yi duk abinda ya dace domin tabbatar da ganin cewa ba’a sake samun irin wannan matsalar rashin biyan albashi ba.
Ministan ya kara da cewa bayan maganar albashi sauran matsalolin da yake addabar ma’aikatan za’a tabbatar da ganin cewa a shawo kansu da kuma tattaunawa da Malaman akai akai.
Your browser doesn’t support HTML5