An Dage Dokar Hana Fita A Babban Birnin Iraqi

Hukumomin kasar Iraqi sun dage dokar hana fita da suka sanya a birnin Baghadaza yau Asabar, dokar da masu zanga zangar kin jinin gwamnati suka bijirewa. Adadin mutanen da aka kashe cikin kwanaki hudu na tashin hankalin da aka yi a kasar ya kai saba’in da biyu, daruruwan mutane kuma sun jikkata.

Zirga zirgar ababen hawa na aiki kamar yadda aka saba a fadin babban birnin na Iraqi da kuma kan tituna, sai dai ko’ina yayi shiru a wasu manyan wurare dake birnin. An sanya shingayen kankare don toshe hanyoyin da dubban masu zanga-zangar suka yi arangama da ‘yan sanda a cikin wannan makon.

Wata hukumar kula da hakkokin bil’adama a Iraqi ta ce jami’an tsaro sun tsare daruruwan jama’a saboda zanga-zangar da suka yi amma sun saki yawancinsu.

Ranar Talatar da ta gabata ne aka fara zanga zangar a Baghadaza akan rashin ayyuka, da muhimman abubuwan more rayuwa, da kuma cin hanci da rashawa a gwamnati, kuma nan da nan zanga zangar ta bazu zuwa wasu biranen Iraqi, musamman a kudancin kasar.