An ji shugaban kungiyan ‘yan tawayen na cewa daga yanzu iyaye ba zasu binne ‘ya ‘yan su maza da mata ba wadan da aka kashe wurin yaki.
Shugaban ‘yan tawayen da ake kira Timosshenko, yace daga yanzu duk wata adawa da rashin jittuwa zata zame tarihi.
Shima shugaban kasar na Colombia Juan Manuel Santos, tuni ya bayyana cewa sojoji zasu ajiye makaman su daga yau Litini.
Yanzu dai duka bangarorin biyu sun bayyana aniyar su ta samar da zaman lafiya a cikin watan da ya shige a Havana wanda ya kawo karshen fadar da aka kwashe shekaru 52 ana gwabzawa tsakanin ‘yan tawaye kasar Colombia masu raayin rikau da kuma gwamnatocin kasar daban-daban. Da suka gabata.
Ana sa ran dai a jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a akan wannan yarjejeniyar ta kasance a cikin watan gobe.
Yakin wanda ya aka fara shi a matsayin bore a shekarar 1964, ya kasaita ya koma yakin da ya lakume rayukan jama'a har sama da dubu 220, kana ya kori mutane kusan miliyan 5 daga muhallin su.