Sojojin da ke dauke da makami na Kasar Sudan ta Kudu dama wadanda basu dauke dashi sun sa hannun a wata yarjejeniyar. Dalilin haka ko shine domin su dakatar da bude wuta.
An cimma wannan yarjejeniyar ce a ranar alhamis din data gabata.
Bangarorin biyu suka ce sunyi imanin cewa wannan karon suna da yakinin zaman lafiya zai dawo cikin kasar.
Suk ace hakan abu ne mai yiyuwa duk ko kin da gwamnati tayi na sake zama a sulhu da ita bayan yarjejeniyar watan Agustan shekarar 2015 da baiyi nasara ba.
Martin Elia Lumoro wanda shine shugaban tawagar gwamnatin Sudan ta Kudu a wannan tattaunawar .
A Kasar Adis Ababa ne aka yi wannan zaman wanda yace an samu muhawara mai zafin gaske tsakanin masu tattaunawar
Ministan Yace sailin da aka fara wannan batu an fara shi ne a mawuyacin yanayi, a majilisar ministocin, amma aka yi nasarar tsallake wannan yanayi.
Haka kuma aka gaza samun matsaya akan batun sayen makamai amma daga bisani aka cimma matsaya, don haka yana ganin an dunfari hanyar cimma matsaya.
Ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu Deng Alor shine yasa hannu a madadin hursunonin kungiyasr SPLM dake tsare a matsayin hursunoni suyasa.
Yace yarjejeniyar wani mataki ne na kaiwa ga ga nasara.
Ministan yace abinda yake yiwa murna shine babban abu a kundin da aka sa hanu a yarjejejiniyar shine dakatar da kaiwa juna hari lokacin da ake wanmnan tattaunawar.
Yace domin wannan ya kara wa mutanen kasar tasu kwarin gwiwa game da wannan batu
Sai dai mai Magana Da yawun National Salvation Front, Yen Mathew yace shikan baya da kwarin gwiwa a wannan yarjejeniya domin a rubuce yana da kyau amma aiwatarwar shine kila ya zame matsala.