Gwamnatin Sudan Ta Kudu da kungiyoyin mayaka sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar tsagaita wuta jiya Alhamis, a yayin tattaunwar zaman lafiya a kasar Habasha, a yinkurinsu na baya-bayan nan na kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru hudu ana yi.
Yarjajjeniyar ta tanaji cewa zuwa gobe Asabar dukkan bangarorin za su kawo karshen gwagwarmaya da makami, su janye daga fagen daga, su saki fursunonin yaki, da ‘yan siyasan da ke tsare, da kuma mata da yaran da aka kama.
Ciyaman din Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya bayyana yarjajjeniyar da abin da ya kira, “matakin farko mai karfafa gwiwa,” a kokarin da ake na kawo karshen yakin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.