An Ci Tarar Lazio Kan Wariyar Launin Fata

Dan wasa Balotelli

An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Lazio kudi euro dubu 20,000, kimanin fam dubu (£16,958) sakamakon nuna wariyar launin fata da magoya bayanta suka yi wa dan wasan gaba, na kungiyar kwallon kafa na Brescia, Mario Balotelli.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da suke fafatawa a gasar "Seria A" na kasar Italiya, inda magoya bayan Lazio suka yi ta rera wakokin batanci na nuna wariyar bakaken fata.

Wasan an tashi Lazio na da ci 2-1 Mario Balotelli ya fara jefa kwallo a ragar Lazio kafin ta rama inda daga nan ne aka fara wakar.

Balotelli mai shekara 29 da haihuwa, ya ce wannan abin kunya ne a wajen magoya bayan Lazio.

Lokacin shari'ar an bukaci wasu karin bayanai daga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Italiya (Italian Football Federation) domin yiwuwar kara wasu takunkumai.

A nata bangaren, kungiyar kwallon kafa ta Lazio, ta yi Allah wadai da wannan hukunci, ta ce kuma ba ta goyan bayan dabi'ar wariyar launin fata, maimakon haka, ya kamata a hukunta magoya bayan da suka aikata laifin ne kawai.