An Ci Gaba Da Zanga Zanga A Kasar Iraqi

Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a babban birnin Iraqi sun toshe manyan hanyoyi a birnin.

An kuma rufe makarantu da ofisoshin gwamnati a Baghadaza da kuma wasu biranen kasar a yau Lahadi, ranar aiki ta farko a mako a kasar da galibin ta musulmai ne, yayinda masu zanga zangar suka hau kan tituna suna neman sauye sauye a tsarin siyasar kasar.

A jiya Asabar masu zanga zangar sun yi gangami inda suka bijirewa matakin da gwamnati ke dauka akan su.

Dubban ‘yan Iraqi sun taru a filin Tahrir dake Baghadaza shekaran jiya Juma’a inda suka gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati mafi girma tun bayan da aka fara zanga zangar a watan da ya gabata.