Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ceto kimanin jarirai da 'yan mata talatin da ake keta hakinsu a jihar Imo
Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya ta ceto wadansu jarirai da kuma ‘yammata da dama a wani gida inda ake tsare mata bayan an yaudare su, sun shiga gidan, a kuma rika yi masu fyade domin su dauki ciki a sayar da jariran da suka haifa.
A cikin hirarsu da manema labarai, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Mohammed Musa Katsina ya bayyana cewa, an shafe shekaru ana keta hakin bil’adama a wannan gidan, wanda aka sawa suna “Green House” ana kuma gudanar da sana’oi a kofar gidan kamar sauran gidajen dake kewaye ba tare da sanin abinda ke gudana a cikin gidan ba.
Bisa ga cewarshi, an sami kananan yara da dama a gidan wadanda dukansu shekarunsu basu wuce sha shida zuwa sha tara ba. Yace an sami jarirai da ‘yammata guda talatin a wannan gidan.
Ga rahoton da wakilinmu a yankin Naija Delta, Lamido Abubakar ya hada mana a kan wannan batun.

Your browser doesn’t support HTML5