Dogarawan tsaron gabar Spain sun ce sun ceto bakin haure sama da 930, sun kuma gano gawarwaki hudu tsakanin ranakun Jumma'a da Asabar a tekun Bahar Rum, a daidai lokacin da kasar ke jiran isowar jirgin gudanar da ayyukan ceto mai suna Aquarius, wanda sananne ne a cikin jerin abubuwan da ake takaddama a kansu a kungiyar tarayyar Turai, kan yadda ya kamata a tinkari matsalar bakin haure.
Dogarawan tsaron gabar sun ce sun ceto daruruwan bakin hauren ne ta wajen amfani da kananan kwale-kwale na balam-balam a mashigar ruwan Gibraltar, inda nan ne ma suka gano gawarwaki hudun.
A halin da ake ciki kuma, kasar Faransa ta yi maraba da tayin da kasar Spain ta yi ma ta, na ansar wasu daga cikin daruruwan bakin hauren da ke cikin jirgin gudanar da ayyukan ceton na Aquarius, wanda a yanzu haka ya doshi kasar ta Spain, bayan da gwamnatin Italiya ta yanzu mai daridari da baki, da kuma kasar Malta su ka hana jirgin tsayawa a gabobinsu ruwansu.
Kasar ta Spain ta fadi cikin wata takardar bayani a jiya Asabar cewa, Faransa ta amince da tayin da ita Spain din ta yi, na sauke bakin haure masu niyyar isa kasar ta Faransa, kuma su ka cika ka'idojin shiga kasar Faransar don neman mafaka.