An Ceto Bakin Haure 211 Daga Tekun Libya

Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure.

Wasu kungiyoyin jinkai sun ceto karin wasu bakin haure a su 81 ruwan Lybia a jiya Lahadi, lamarin da ya kai adadin mutanen da aka cetosu daga teku tun ranar Juma’a zuwa 211.

Kungiyar “Doctors without Borders” da hadin gwiwar kungiyar SOS Mediterranean sun yi aikin ceton ne da wani jin ruwa mai dauke da tutar kasarNorway mai suna Ocean Viking.

Akasarin mutanen da aka ceto tsakanin kwanaki uku, ‘yan maza ne daga kasar Sudan, ciki har da mutane 81 da aka samo su a cikin wani karamin kwalekwalen roba. Ma’aikatan jirgin ruwan “Ocean Vinking” da suka shedi al’amarin sun ce mutanen da suke cikin kwalekwalen robar da ya sace, sun barke da murna a lokacin da su ka ga masu ceton.