Mukaddashin kakakin hedkwatar 'yan sandan Najeriya Aremu Adenweron ya nunawa 'yan jarida wasu 'yan fashi da makami da a ranar 12 ga watran Disambar bara suka kai farmaki gonar shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu dake wajen Abuja, inda suka bindige wani dan sanda dake gadi a gonar.
Jagoran 'yan fashin, yayi karin bayani akan yadda suka tsara aika aikar, yace abokin shi ne ya kirashi yace Ibrahim Magu ya boye kudi a soakaway a gidan sa sai ochife yace ya san wasu sojojin sama biyu, da zasu taimaka wajen debo wadannan kudade, sunaso su samu rabon su a cikin ganimar kasar tinda wahala tayi yswa.
Daya daga cikin su mai suna Vincent Micheal korarren sojan saman Najeriya ne shine ya gayyato wasu sojojin sama biyu daga cikin bariki wadanda suka tsara suka shiga suka dauke hankalin jami'an 'yan sandan har suka daddaure su, sauran kuma suka shiga gonar tare da fasa saokaway amman basu ga komai a ciki ba, shine suka kwace bindigogin su suka tafi dasu Benue domin su saidasu akan Naira dubu 400 kowanne.
Rundunar 'yan sandan tace ta samo bindigogin ';yan sandan nata guda biyu, da harsasai guda 60 da wayar salular su, su kuma sauran sojin saman guda biyu da aka aikata wannan fashi dasu, ance yanzu haka suna hannun rundunar sojin saman suna fuskantar bincike irin na cikin gida, bayan nan za a mika su ga rundunar 'yan sanda dga bisani kuma a gurfanar dasu a gaban kotu.