An Cafke Wata Mata Mai Safarar Yara A Jihar Inugu

Wadansu kananan yara suna wasa.

'Yan sanda a jihar Inugu sun ce sun cafke wata mata bisa zargin sace wani yaro mai shekaru 7 daga Zaria da ke jihar Kaduna, da aniyar sayar da shi a jihar Inugun, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Inugu Mista Daniel Ekea ya shaida.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, a ranar 9 ga watan Afrilun wannan shekarar 2022, rundunar 'yan sandan jihar Inugu ta kama matar da ake zargi, mai suna Juliet Donatus mai shekaru 35, 'yar asalin jihar Imo, amma mazauniyar Zaria jihar Kaduna.

An kama ta ne bayan wani bayanin sirrin da aka samu da ke zargin cewa an same ta da wani yaro, kuma ta kasa bada bayani mai gamsarwa akan zargin.

An tura batun ga sashen bincike na rundunar 'yan sandan jihar, inda ake gudanar da bincike akansa, kuma a halin yanzu, bincike ya nuna cewa ta sace yaron ne daga Zaria ta kawo shi Inugu.

Ku Duba Wannan Ma Ana Zargin Tsohuwa ‘Yar Shekaru 100 Da Yin Sanadin Kwakule Idon Almajiri

An kama ta ne yayin da ta ke kokarin sayar da yaron, kuma yanzu hakan rundunar 'yan sandan jihar tana kokarin ganin an maida batun zuwa rundunar 'yan sandan jihar Kaduna.

Hukumomi sun samu iyayen yaron wadanda su ka isa garin Inugu doin tantance yaron, kafin su koma da shi gida.

Saurari rahoto cikin sauti daga Alphonsus Okoroigwe:

Your browser doesn’t support HTML5

An Cafke Wata Mata Mai Kokarin Safarar Wani Yaro A Jihar Inugu