Fashi da makami da satar dabbobi da kuma yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a jihar Neja, dake yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.
Tuni dai wannan matsala ta jefa, jama’a, da dama cikin yanayi na tashin hankali.
Abdullahi Yarima tsohon shugaban karamar hukumar Shiroro, yace “A ‘yan kwanakin nan sun sace wata yariya amma Allah ya kubutar da ita sun kuma kashe wani matashi mai suna Danladi Sabon kudu a garin Bassa, sun kuma kwashi garke biyu nan a wani Bafulatani mai suna dan Dare, yanzu haka muna cikin zullumi ,muna kira ga Gwamnati da ta tamaka domin magance mana wannan matsalar.”
A kan wannan matsala dai majalisar dokokin jihar Nejan, ta kira Kwamishina ‘yan sandan jihar domin sanin matakan da suke dauka akan wannan matsala.
Rundunar ‘yan Sandan jihar tace tana iya kokari domin a yanzu haka rundunar ta samu nasarar cafke wasu daga cikin masu wannan ta'annati, inji kakakin ‘yan Sanda Mr. Bala El-kana.
Ya kara da cewa sun kama mutane talatin sun kuma samu kwato shanu dari shida sun kuma maidawa masu shi.