Rundunan tsaron farin kaya ta 'Cibil Defense' a Najeriya, ta ce ta yi cafke wasu da ake zargin barayin shanu ne a jihar Taraba da ke Arewa maso gabashin Najeriya.
Dubun barayin dabbobin ta cika ne bayan wani samame da jami’an suka kai a mabuyar bata garin.
Yanzu haka dai matsalar satar shanu da kuma kananan dabbobi, baya ga satar jama'a domin neman kudin fansa, na cikin matsalolin da ke addabar al'ummar jihar Taraba.
Sai dai hukumomin tsaro a jihar sun ce sun tashi tsaye domin yaki da wannan annobar, inda hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defense, ta samu nasarar cafke wasu barayin shanu.
Daga cikin wadanda ake zargi da satar shanun har da Umar Buba mai shekaru 37.
Har ila yau akwai wani mai suna Peter, wanda ke amfani da Keke Napep wajen satar kananan dabbobi.
Da yake yi wa manema labarai bayani na irin nasarorin da suke samu a yanzu, kwamandan rundunan tsaron farin kaya a jihar Taraban Isa Kamilu, ya ce za su ci gaba da kokarin da suke yi na kare dukiyoyin gwamnati da na al'umma.
Haka nan kuma kwamandan ya shawarci al'umma da su ci gaba da sa ido da kuma ba su bayanai na duk wasu abubuwan rashin gaskiya da suka gani.
Your browser doesn’t support HTML5