Kakakin rundunar 'yan sandan Nigeria, Jimoh Moshood, ya sanar da cafke gungun barayin da suka kashe mutane akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, da suka hada da Farfesa Halima Sa'adiya Idris, tsohuwar kwamishaniyar ilimi ta jihar Katsina.
Cikin wadanda aka kara cafke wa har da 'yan fashi da makamin da suka afka gidan daraktan cibiyar binciken ayyukan gona ta Jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Kalib Uthman, inda suka yi garkuwa da wata mata mai jego tare da jaririnta.
Speto Janar na 'yan sandan Nigeria Alhaji Ibrahim Idris, ya kuma umurci duk 'yan sandan kwantar da tarzoma dake jihar Kaduna da yanzu suke waje su gaggauta su koma Kadunan domin samar da cikakken tsaro a jihar.
Shuaibu Mungadi wani mai sharhi akan alamuran 'yan sanda a Nigeria, ya ce idan mutanen da aka kama su ne suka aikata laifin to ana iya cewa 'yan sandan sun cancanci yabo. Idan kuma rashin kayan aiki ne ya sa sai an aikata laifi suke yunkura to ya kamata a samar masu da isassun kayan aiki.
A cewar Mungadi ana zarge zarge da yawa akan ayyukan 'yan sanda a kasar saboda sau tari su kan kama mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a dora masu laifi da zummar samun yabo daga al'umma ko kuma su fitar da kansu daga zargin gwamnati.
Akwai zargin cewa 'yan sandan nada bata gari da yawa a cikinsu dake aikata miyagun ayyukan dake faruwa. An sha samun bata garin amma ba'a jin matakin da hukumar 'yan sandan take dauka a kansu.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5