An Bullo da Wani Shiri na Talafawa Mata Masu Juna Biyu a Jihar Bauchi

Wata uwa ta na rike da dan ta ana yi mi shi allurar rigakafi

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta bullo da wani shiri na talafawa mata masu juna biyu domin kula da kansu lokacin da suke da juna biyu da lokacin haihuwa, da kuma yiwa 'ya'yansu rigakafi.
Gwamnatin tarrayar Najeriya ta bullo da wani shiri na talafawa mata masu juna biyu domin kula da kansu lokacin da suke da juna biyu da lokacin haihuwa, da kuma yiwa 'ya'yansu rigakafi.

Mata masu juna biyu a jihar Bauchi sun bayanna anfanin talafin da shirin rarar kudin man fetir ya bayar a bangaren kiwon lafiyar su.

Maryam Mohammed, wata mace a jihar Bauchi da ta ci moriyar shirin ta bayanna farin cikinta game da wanan shirin. Tace, "Da, bai fi a yi ma mutum kaman ashirin ko makamancin haka ba amma yanzu, mata suna zuwa sun fi mutum dari saboda suna samun cin gajiyan wannan shirin da ake yi."

An bayana cewa shirin yana bi daki daki ne, tunda ga fara awo zuwa haihuwa da rigakafi.

Ga cikakken rahoton da wakiliyar Sashen Hausa, Amina Abdulahi Girbo ta hada.

Your browser doesn’t support HTML5

Kiwon lafiya a Bauchi - 2:10