Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton tayi kira ga kasashen Sudan da Sudan ta kudu dasu magance sabani ko kuma rikice rikicen da suke tsakaninsu, wadanda suka sa sauran kiris su tsunduma kasashen cikin yakin basasa.
Yau juma'a Hillary Clinton ta zanta da yan jarida bayan yar ziyarar data kai Juba, baban birnin Sudan ta kudu,. inda ta gana da shugaban kasar Salva Kir.
Tace tilas Sudan da Sudan ta kudu suyi da wajewa domin magance sauran batutuwa a tsakaninsu, musamma ma tayi kira ga bangarorin da suyi wa Allah sun cimma yarjejeniyar akan yada zasu raba kudi da aka samu daga cinnikin mai.
A watan Janairu Sudan ta kudu ta dakatar da dukkan aiyukan hakar mai, a saboda rikici tsakaninta da kasar Sudan akan kudin da aka bukaci ta biya domin tana amfani da bututun man Sudan. Yau Juma'a Mrs Clinton tace kodayake kasashen biyu, kowa ya kama gabansa, to amma makomarsu da arzikinsu basu taba rabuwa ba.
Yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa kasashen wa'adin kan ranar biyu ga wannan wata na Augusta su magance sabaninsu ko kuma a aza musu takunkunmi. Alhamis wannan wa'adi ya cika ba tare da kasashen biyu sun cimma daidaituwa ba.
Sabanin dake tsakanin kasashen biyu yana jawo barazanar gurgunta tattalin arzikin kasashen biyu