A yayin da ga dukkan alamu abubuwa ke dada yin yawa ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kuma ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar karanci da kuma tsadar man fetur da kuma, uwa-uba, abubuwan da ke bin bayan tsada da kuma rashin man, gamayyar kungiyoyin sa kai a Kano sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta sauka daga kujerar Ministan Albarkatun Mai na kasar kuma ya nada wanda ya kamata domin tunkarar wannan matsala.
Su ka ce idan aka nada Ministan mai, za a san wanda za a tambaya idan aka samu matsala a maimakon Shugaban kasa, wanda akwai abubuwa da yawa gabansa.
A wani taron gaggawa dangane da halin da kasa ke ciki, kungiyoyin sun tattauna sauran batutuwa da suka shafi rayuwar Jama’a, musamman hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma yawaitar rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, lamarin da sukace na kara zama barazana ga makomar Najeriya.
Dr Muhammad Mustafa Yahya, Daraktan Kungiyar Democratic Action Group shine yayi Magana da manema labarai a madadin sauran kungiyoyin, kuma ya yi wa wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari Karin haske game da abubuwan da taron ya cimma. Ga dai kwari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5