An Bukaci a Nisanta Addini daga Bakar Akidar Boko Haram

Sakataren Kungiyar Kiristocin Najeriya Rabaran Musa Asake da Shugaban Kungiyar IZALA Shaikh Abdullahi Bala Lau a wurin kallon majigin da VOA ta shirya akan Boko Haram

Yayinda ake ci gaba da nuna majigin Muryar Amurka akan Boko Haram mai taken Tattaki daga Bakar Akida shugabannin addini sun bukaci a nisanta addini da akidar Boko Haran tare da kiran hadin kai tsakanin Kirista da Muslmi a Najeriya

A lokacinda ake nuna majigin Muryar Amurka kan yaki da bakar akidar Boko Haram malamai da kungiyoyin matasa sun nuna bukatar a bude sabon babi na nisanta addini daga muguwar masu kashe jama’a ba tare hakkin shari’a ba.

Shugaban kungiyar IZALA Abdullahi Bala Lau da sakataren kungiyar Kiristoci ta Najeriya Rabaran Musa Asake sun nuna takaicin yadda ‘Yan Boko Haram suka cuci al’ummar da basu da laifin komi.

Musa Asake, Aliyu Mustapha da Shaikh Bala Lau

Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci cewa a karantar da akida mai kyau. Yayi misali da irin gudummawar da Shaikh Jaafar Mahmud Adam ya bayar da har ya kai ga yi masa kisan gilla. Y ace duk wani malami kuma da yayi yunkurin yin wa’azi akan akidar Boko Haram sai a kasheshi. Dalili ke nan malamai da yawa sun tsorata basa iya fitowa fili su kalubalanci kungiyar Boko Haram ba.

Shi ma Rabaran Musa Asake ya nuna damuwa da yadda ya ce gwamnati tayi sakaci da yaki da Boko Haram tare da cewa majigin na VOA ya fadakar dashi akan bukatar dake akwai Kiristoci da Musulmai su hada kai wajen wanzar da zaman lafiya. Yace da shugabannin addinan biyu sun zauna akan matsalar Boko Haram da sun yi maganin kungiyar. A cewarsa yanzu idan mutum yayi magana sai a bishi ana neman a kasheshi.

Kungiyar matasan Najeriya karkashin shugabancin Murtala Garba da wasu sun halarci taron.

Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da karin baani

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci a Nisanta Addini daga Bakar Akidar Boko Haram - 3' 00"