Kungiyar ‘Yan Mata da ake kira da turanci “Girls Brigade” ta jihar Filato, ta gudanar da bikin “Ranar ‘Ya’ya Mata” da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe inda ta jaddadawa iyaye da mahukunta cewa baiwa ‘ya’ya mata ilmi shi ne ginshikin samar da ‘yan kasa nagari.
Shugabar makarantar Sakandaren Gwaji ta ‘yan mata dake garin Mista Ali a jihar Filato, Malama Mairo Jakada, tace yara mata suna fuskantar matsaloli da dama da suka hada da auren dole, rashin ilmi da matsanancin talauci. Tace sau tari iyaye maza sun gwammace su sa ‘ya’ya maza makaranta yayinda suke tura matan auren dole.
Alkalumma dai sun nuna cewa yara mata sama da miliyan 75 a fadin duniya ke fama da rashin ilmin zamani, yayinda daukan ciki ke hallaka yara mata ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 19 a kasashe masu raunin tattalin arziki
Kwamishaniyar kungiyar “Girls Brigade” ta jihar, Madam Choji, tace manufar ranar ita don a dada fadakar da al’umma gameda martabar ‘yan mata ne.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5