An Bukaci Buhari Ya Binciki Gwamnoni Kan Yadda Suka Kashe Kudade

Shugaba Muhammad Buhari

Kimanin Naira miliyan dubu dari biyar ne gwamnatin Buhari ta ba ma jihohi domin biyan wasu bukatunsu to sai dai wai an soma gano wasu cikin kudaden a wuraren da ba su kamata ba

A kokarin da yayi na fadakar da mutane akan yadda gwamnatinsa ke kashe kudi, gwamnan jihar Adamawa Alhaji Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla yace lokacin da ya karbi mulki babu hanyoyi a jihar saboda haka dole ne ya mayar da hankali akan ginasu domin a samu cigaba.

A cewarsa idan ba'a gina hanyoyi ba tare da wasu abubuwa babu cigaba kuma masu saka jari ba ma zasu yi tunanen jihar ba balantana har su nemi saka jari. Idan kuma babu masu saka jari ba za'a kirkiro ma matasa ayyukan yi ba. Yace sun karbi mulki ne domin su yiwa wadanda suka zabesu aiki ba su cimma muradun kansu ba.

To saidai duk ikirarin da gwamnonin keyi na yiwa mutanensu aiki da kudin da gwamnatin tarayya ta basu akwai wadanda suke ganin ba haka batun yake ba.Onarebul Abdullahi Terembe tsohon kwamishsnan yada labarai a jihar Adamawa yana ganin akwai bukatar Shugaba Buhari ya binciki gwamnoni akan yadda suka kashe kudin Paris Club da ya raba masu.

Yana mai cewa har yanzu "bani da kwarin gwuiwa zasu yi anfani dashi ta wannan wurin saboda kudaden da aka basu a can baya akwai wasunsu da basu yi anfani dasu ba ta hanyar da ta dace".

Inji Terembe tunda ba'a yiwa gwamnonin wani hukumci ba yanzu ma idan sun samu wani sabon kaso zasu yi anfani dashi ne yadda suka ga dama saboda bisa ga shari'a suna da kariya, ba'a isa a tursasasu ba. Dalili ke nan da wasunsu ke maganganun da suka ga dama akan kudaden. Yace yawancin gwamnonin sun zo kasuwanci ne.

Misali an ji gwamnatin Adamawa tana cewa ba za'a tilasta mata yadda zata kashe kudin ba. To saidai kwamishanan yada labarai na jihar yace ba haka batun yake ba tare da cewa an juya abun da suka fada ne.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci Buhari Ya Binciki Gwamnoni Kan Yadda Suka Kashe Kudaden da Aka Basu - 3' 19"