An Bukaci Boko Haram Ta Zauna A Tattauna Da Ita - Idan Tana Da Hujja

Barnar da Boko Haram tayi wa garin Izghe, Fabrairu 15, 2014.

A wurin taron masana kare hakkin bil Adama na duniya a Najeriya, shugaba Jonathan yace damuwar da suka yi da batun yadda sojoji ke tinkarar rikicin Boko Haram
Shugaba Goodluck Jonathan ya sake yin kira ga 'yan Boko Haram da su rungumi tattaunawa maimakon kashe-kashe da tayar da hankalin da suke yi wajen warware duk abinda ke damunsu.

Shugaba Jonathan yayi wannan kira a wurin wani taro na musamman na masana harkokin kare hakkin bil Adama a duniya, wanda ofishin mai ba shugaba shawara kan harkokin tsaron kasa da kuma ma'aikatar shari'ar Najeriya suka shirya da nufin tattauna yadda za a kyautata kare hakki a wuraren da ake fama da fitina.

Wadanda suka halarci taron sun hada har da babbar lauya mai gabatar da kararraki a kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya, Fatou Bensouda.

Wakilinmu Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Tazo A Zauna A Tattauna In Ji Jonathan - 3'06"