An budewa tawagar tsaron Majalisar Dinkin Duniya wuta aka kuma tada nakiya a daidai lokacin da suke kokarin gudanar da bincike da jirgin leken asiri a wani gari dake Syria lokacin da suke dakon ziyarar masu binciken makaman guba.
Da issar su zangon na farko, mutane dayawa sun taru, kuma shawarar da hukumar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta bayar ita ce, tawagar ta janye, bisa ga cewar shugaban kungiyar haramta amfani da makamai masu guba (OPCW) Ahmet Uzumcu jiya Laraba. zango na biyu kuma, tawagar ta fuskanci 'yan harbe harbe, aka kuma tada nakiya a gurin.
Yace lamarin ya faru ne jiya Talata kuma tawagar ta koma Damascus.
Majiya daga Majalisar Dinkin Duniya ta shaidawa VOA cewa, ba wani mamban tawagar da ya ji rauni lokacin aukuwar lamarin.