An bude wata kasuwar dabbobi ta kasa da kasa a yankin kudu maso gabashin Najeriya, koda yake dai a da kasuwar tana wani shashe ne dake jihar Abia, sakamakon rigiggimu da rashi tsaro shi yasa kasuwar ta nufi durkushewa amma yanzu kasuwar ta farfado, kuma ta koma garin Okigwe, dake jihar Imo.
Shuwagabanin wannan kasuwa na jiha dana kasa sun hallar domin tabbatar da cewa wannan kasuwar ta tabbata kuma manyan da kananan sun yi jawabai.
Shugaban masu hada hadar dabbobi na kasa Auwal Ahmed Maiha, yace rashin tsaro, da kulawa da dukiyar mutane da rayukansu wanda kuma ya kasance ginshikin raka rayuwar dan Adam, kasancewar tabbacin tsaro da Gwamnan jihar Rochas Okorocha, ya bada yasa suka dawo Okigwe.
Dangane da maganar tsaro Haliru Gwandu, Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Edo, yace jama’a, su gane cewa jiya ba yau ba idan har akwai wasu batya gari, wadanda suke ganin sun isa suna iya kawo wata barazana toh, su kwance zanin su domin a cewarsa duk wani bata gari zasu sa kafar wando daya dashi.
Your browser doesn’t support HTML5