An Bude Taron Kasashen Gabar Tekun Guinea a Legas

Taswirar yankin Gabar Tekun Guinea

An bude taron kasashen da ke gabar tekun Guinea a Legas domin tattauna matsalolin da ke addabar yankin.

Ministan tsaron Najeriya BrigadierJanar Mansur Dan Ali shi ya bude taron tsaron na kasashe bakwai na yankin gabar tekun Guinea tare da kasashen turai da suka kasance kawayensu.

A cikin jawabinsa ya shaidawa mahalarta taron kokarin da Najeriya da sauran kasashen shida da ke yankin su ke yi na inganta tsaro a yankin.

Ya ce yankin tekun na cike da hadari bisa ga la'akari da ayyukan ta'addanci kamar fashi akan tekun da fasa bututun mai da garkuwa da mutane.

"Kowane lokaci kasashen yankin tekun da kawayensu sukan taru su yi nazari akan abubuwan da ke faruwa, musamman abubuwan da ke da alaka da rashin tsaro kan tekun sannan a lalubo bakin zaren abinda yakamata a yi."

Dangane da ko kungiyar na samun hadin kan kasashen, Janar Mansur Dan Ali ya ce kasancewar kasashe 22 a taron Najeriya, alama ce ta samun hadin kai.

Ga rahoton Babangida Jibrin da kaein bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bude Taron Kasashen Gabar Tekun Guinea a Legas- 3' 05"