Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno, ya bayyana cewa gurin gwamnatinsa ne ta ga cewa dukkan 'yan gudun hijira dake fadin jihar sun koma cikin gidajensu nan da karshen watan Disamba.
Gwamnan yace su na kokarin ganin cewa an dauki matakan gyara muhallan 'yan gudun hijirar tare da samar musu da abubuwan yi ta yadda zasu iya komawa su zauna cikin mutunci da ruyfin asiri a tsakanin iyalai da 'yan'uwa a garuruwansu.
Gwamna Kashim Shettima yana bayyana wannan ne a lokacin da ake bude wasu gine-ginen gwamnati da aka sake ginawa a garin Dikwa, tare da taimakon Kwamitin tallafawa 'yan gudun hijira na kasa dake karkashin jagorancin Janar Theopilus Danjuma mai ritaya.
A bayan da sojoji suka kwato garin na Dikwa, kwamitin TY Danjuma ya bada gudumawar Naira miliyan 25 domin sake gina makarantu, asibitoci da kuma sakatariyar karamar hukuma.
A jawabinsa wajen bukin, Janar Danjuma yace kimanin rabin kudaden da aka yi alkawarin bayarwa agaji ga wannan kwamitin ne kawai ya shiga hannunsu, amma su na bakin kokarinsu na tabbatar da cewa sun yi amfani da abubuwan da suka samu domin kyautata rayuwar 'yan gudun hijirar.
Jama'a da dama sun bayyana farin cikinsu da wannan kokari, sun kuma yi rokon da a kara azama wajen tallafawa wadanda suka rasa komai nasu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri...
Your browser doesn’t support HTML5