An bindige Janar Kararuza mai ba shugaban kasar Burundi shawara

Cikin motar da aka kashe Janar Athanase Kararuza a Bujumbura babban birnin Burundi

An bindige wani Janar din Soja har lahira a Burundi jiya Litinin lokacin da yake kokarin sauke ‘yarsa a makaranta. Wannan abu ya zo daidai lokacin da Kotun Hukunta Laifuffukan Yaki ta duniya tace zata sawa kasar ido game da yawan barkewar rikici.

An kashe mashawarcin shugaban kasar Burundin ne Janar Athanase Kararuza tare da matarsa da daya daga cikin masu tsaronsa a Bujumbura babban birnin kasar, har ita ‘yar tasa ta ji rauni a wannan hari da ya faru a gaban makarantarsu.

Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi Allah wadai da wannan harin da aka kaiwa Janar din, wanda ya taba aiki da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kakakin Magatakardar Stephane Dujarric yace, ire-iren wadannan rikicin ba a bin da zai karawa kasar ta Burundi face kara uzurra rikicin da kasar ke ta fama da shi. Yace Sakataren MDD ya yi kiran da ayi bincike game da wannan farmakin.

Ba dai wanda ya dauki alhakin kai wannan harin ya zuwa yanzu. Rikicin dai tsakanin magoya bayan Shugaban Kasar Pierre Nkurunziza da magoya bayan abokan adawarsa ya faro ne tun a watan Afrilun shekarar 2015.

Lokacin da shugaba Nkurunziza ya sanar da neman tazarcen sa karo na 3 na mulkin kasar, wanda ake kallo a matsayin abinda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Tun daga nan ake ta kaiwa juna harin sari ka noke ga sojoji, ‘yan siyasa da shugabannin kungiyoyin fararen hula.